Yaronka ya na buƙatar shan maganin da ake ƙira hydroxyurea. Wannan takardar bayanin ta na bayyana abin da hydroxyurea ya ke yi da kuma yadda ake ba yaronka wannan magani. Hakanan ta na bayyana yadda zai iya samun wasu matsaloli ko illoli yayin da ya ke amfani da wannan magani.
Menene hydroxyurea?
Hydroxyurea magani ne na kemotherafy da ake amfani da shi wajen magance wasu cututtuka, ciki har da cutar sikila. Bincike ya nuna cewa marasa lafiya da ke ɗauke da cutar sikila da ke amfani da hydroxyurea suna:
- zuwa asibiti saboda abubuwan da suka faru masu raɗaɗi rabinsu kawai kwatankwacin marasa lafiya da ba sa amfani da hydroxyurea
- samun lokuta kaɗan cikin damuwa na ciwon ƙirji mai tsanani.
- samun ƙarancin buƙatar ƙarin jini idan an kwantar da su a asibiti
Za ka iya jin ana ƙiran hydroxyurea da sunan alama, Hydrea. Hydroxyurea ya na zuwa cikin nau'in ƙwayar magani (capsule).
Za a iya bayar da hydroxyurea ga yaronka idan:
- an kwantar da shi asibiti sau uku ko fiye da haka don wasu lokuta masu raɗaɗi a cikin watanni 12 da suka gabata
- sun buƙaci musanyan jini sau ɗaya ko fiye da haka a lokuta na ciwon ƙirji mai tsanani
- sun ɗauki lokaci mai mahimmanci daga makaranta ko aiki saboda raɗaɗi da dama da ke faruwa a gida
Kafin a ba yaronka hydroxyurea
Faɗawa likitan yaronka idan yaronka ya na da matsala ko rashin jituwa da wani sinadari na hydroxyurea ko wani abu da aka haɗa shi da shi ko kuma ya na da wata cuta ko matsala ta jini (banda cutar sikila).
Yi magana da likitan yaronka ko mai haɗa magani idan yaronka na da wani daga cikin waɗannan yanayi. Dole ne a ɗauki matakan kiyayewa idan:
- ya na da ciwon hanta
- ya na da ciwon ƙoda
- ta na iya kasancewa mai ciki (idan yariya ce)
Yadda ake ba yaronka hydroxyurea?
- Ka ba yaronka hydroxyurea kamar yadda likitanka ko mai haɗa magani ya ce ka yi. Ka yi magana da likitan yaronka kafin ka dakatar da wannan magani ko don wani dalili. Zai iya ɗaukar wasu watanni kafin a ga cikakken tasirin maganin.
- Ana iya yin gwajin jini duk bayan wata biyu lokacin fara amfani da wannan magani don samun madaidaicin ƙwayar da ta dace da yaronka.
- Ka ba yaronka hydroxyurea sau ɗaya a rana, a kusan lokaci guda kowace rana. Wasu marasa lafiya sun fi son sha lokacin kwanciya.
- Za ka iya ba da hydroxyurea tare ko ba tare da abinci ba. Bayar da shi da abinci na iya taimakawa wajen hana ciwon ciki.
- Ya kamata yaronka ya sha ruwa sosai ko wace rana.
- Idan yaronka ya yi amai ƙasa da rabin sa’a bayan shan hydroxyurea, ka ba shi wani sashi na maganin. Idan ya yi amai fiye da rabin sa’a bayan shan hydroxyurea, kada ka ba shi wani sashi. Ka ba shi na rana mai zuwa a lokaci na yau da kullum.
- Hydroxyurea ya na zuwa a matsayin ƙwaya mai gram 500 a Kanada. Yaronka ya kamata ya haɗiye ƙwayar maganin duka tare da kofi na ruwa ko wani abu na ruwa.
- Idan yaronka ba zai iya haɗiyar ƙwaya ba ko ya na buƙatar sashi ƙasa da kwaya ɗaya, ka tattauna da mai haɗa magani yadda ya kamata a ba shi. Ana iya buɗe ƙwayar a jefa cikin sirinjin magani domin bayar da sashin da aka rubuta. Ka zubar da maganin da ya rage.
- Mai haɗa magani zai koya maka yadda za ka sarrafa hydroxyurea lafiya, gami da amfani da sáfar hannu lokacin haɗawa da foda daga cikin ƙwaya. Haka kuma zai nuna maka yadda za ka zubar da maganin lafiya.
- Duk wanda zai sarrafa hydroxyurea ya kamata ya wanke hannunsa kafin da bayan taɓa kwalba ko ƙwaya. Don cikakken bayani kan sarrafa hydroxyurea a gida, duba Kemotherafy a gida: Yadda ake bayar da ƙwayoyi ga yaronka a tsanake.
Menene ya kamata ka yi idan yaronka ya manta da shan hydroxyurea?
- Idan ya manta, kada ka bayar da ƙarin sashi akai don cike wancan.
Zuwa yaushe hydroxyurea zai fara aiki?
Zai iya ɗaukar wasu watanni kafin a ga canji a gwajin jini.
Menene illolin hydroxyurea da yadda ake lura da su?
Yaronka na iya samun wasu daga cikin waɗannan illoli yayin da ya ke amfani da hydroxyurea. Ka tuntuɓi likitan yaronka idan yaronka ya cigaba da samun waɗannan illolin kuma ba su tafi ba, ko sun dame shi:
- Amai: A nisanci shan hydroxyurea al halin babu abinci.
- Fari ko ɗan kumburi a fata: Wannan zai iya wucewa bayan wani lokaci ko da an cigaba da amfani da maganin. Idan ƙurji ya fito, duba likitan da ya rubuta hydroxyurea ga yaronku.
- Zubewar gashi: Wannan ya na faruwa amma ba ya kaiwa ga kaurin gashi sosai. Idan hakan ya faru, ana buƙatar ka yi magana da likitan yaronka don yanke shawara kan ci gaba da amfani da maganin.
- Rage wasu ƙwayoyin jini: Yaronka na buƙatar gwajin jini ko wace wata biyu na shekara ta farko ta magani. Ana iya yin waɗannan gwaje-gwajen a ɗakin gwaje-gwaje na gida kuma ana aika sakamakon zuwa likitan ɗanku. Idan ƙididdigar ta kasance ƙasa da ƙayyadaddun matakin yarda, za a ƙira ku don riƙe maganin kuma ku maimaita gwajin jini cikin kwanaki bakwai. Yawan adadin yakan warke kuma ana iya ci gaba da maganin kamar yadda aka tsara. Idan adadin farar jinin halitta ya sake faɗuwa, to, za a rage adadin zuwa adadin da yaronka ya yi kafin ƙidayar ta fara faɗuwa. Yaronka zai ci gaba da shan wannan ƙananan sashi.
- Duhu a fata da farce: Bayan shan hydroxyurea na wani lokaci, wasu marasa lafiya na samun duhun farce da fata a wurare kamar gwiwar yatsu. Wannan yana wucewa bayan an daina maganin.
- Matsalar hanta (lafiya): Wannan ba ya faruwa a kullum, amma ana yin gwaji ko wani wata uku don wannan.
- Ciwon kai.
- Raunin tsoka, musamman a cinyoyi da hannuwa.
- Farin baki ko kumburi: Yi amfani da buroshin wanke baki mai laushi da ɗauraye bakin zai taimaka.
- Tasirin dogon lokaci: Hydroxyurea magani ne na chemotherapy, kuma wasu nau'ikan magungunan na da alaka da marasa lafiya da ke fama da ciwon daji tsawon shekaru masu yawa. Amma a cikin fiye da shekaru 20 na amfani da hydroxyurea a cikin masu cutar sikila, ba a sami rahoton wannan maganin na haifar da ciwon daji ba.
Mainene Matakan Kiyayewa Yayin da Yaronka Ya ke Amfani da Hydroxyurea?
Hydroxyurea na iya rage yawan ƙwayoyin jini na ɗan lokaci, wanda zai iya sa yaronka cikin haɗarin kamuwa da cututtuka. Don kare yaronka daga kamuwa da cuta, ya na da kyau ya guji mutane da ke da cututtuka irin su mura ko zazzaɓin sanyi, musamman idan ƙwayoyin jininsa su yi ƙasa.
Akwai yiwuwar hydroxyurea na iya haifar da matsalolin haihuwa idan aka sha lokacin ɗaukar ciki ko a lokacin juna biyu. Idan ki na cikin shekarun haihuwa kuma ki na shan hydroxyurea, ana ba da shawarar yin amfani da wata hanyar kariya daga ɗaukar ciki. Idan ki ka samu ciki yayin shan hydroxyurea, ya kamata ki dakatar da maganin nan-da-nan kuma ki sanar da likitanki.
Dole ne a dakatar da shan hydroxyurea na a ƙalla watanni uku kafin yunƙurin samun ciki. Hakanan, hydroxyurea na iya rage yawan maniyyin maza.
Idan yaronka ya na da HIV kuma ya na shan magani don wannan cutar, musamman didanosine ko stavudine, ka tuntuɓi likitan yaronka.
Wannan ba cikakken jerin bayanai ba ne. Tabbatar da ka tattauna da likitan yaronka ko mai haɗa magani kafin ba shi wasu magunguna (na rubutu ko na ganye ko kayan halitta).
A matsayinka na mahaifi ko mai kula, haɗarin lalacewa daga sarrafa magunguna masu haɗari ƙanana ne, amma ya na da kyau a rage ko a guji kusanci da shi. Wannan ya haɗa da gujewa ɗanɗana maganin yaronka. Haka kuma, idan kina da juna biyu ko ki na shayarwa, ya na da kyau ki guji hulɗa da wannan magani mai haɗari. Idan zai yiwu, ki nemi wani ya ba yaronki maganinsa.
Magunguna masu haɗari na iya cutar da ƙwayoyin jiki masu lafiya. Duk wanda zai taɓa irin wannan magani mai haɗari ya kamata ya kare kansa. Ka na iya amfani da safar hannu da abin rufe fuska lokacin sarrafa maganin yaronka. Haka kuma, kafin ka fara shirya maganin yaronka, ka wanke hannunka da sabulu da ruwa.
Wani muhimmin bayani ya kamata ku sani game da hydroxyurea?
- Dole ne a sha wannan magani kullum, ba kawai a lokacin da zafi ya fara ba. Ba zai cire zafin a lokacin da ake jin shi ba. Ya na aiki ta hanyar canza jinin, wanda ke hana aukuwar zafin. Ya na rage yawan zafin, rage fashewar jini, da ƙara kariyar fetal hemoglobin.
- A ziyarar watanni ɗaya, ana ganin jan jini ya fi girma. Wannan ana iya ganinsa a gwaje-gwaje ko a ƙarƙashin microscope. Wannan jinin ya na iya wucewa cikin ƙananan jijiyoyin jini cikin sauƙi kuma ba ya fashewa cikin sauƙi. Iyayen sukan lura da cewa yaron ya kara cin abinci.
- Bayan watanni uku da shan maganin, ya na ƙara fetal hemoglobin da hemoglobin gaba ɗaya. Mun san cewa marasa lafiya da ke da yawan fetal hemoglobin su na da ƙarancin lokutan zafin.
- Bayan watanni shida, ya kamata yaronka ya sami ƙarancin zafin fiye da yadda yake kafin fara maganin.
- Yawan lokacin da za a ci gaba da shan wannan magani zai zama shawara tsakanin marar lafiya da likitansa.
- Hydroxyurea ya na cikin tsarin inshorar lafiya da kuma tsarin Ontario Drug Benefit.
- Kada a raba maganin yaronka da wani. Kada kuma ka ba yaronka maganin wani.
- Ku tabbata ku na da isasshen hydroxyurea don ya isa zuwa ƙarshen mako, hutu, da kuma tafiye-tafiye. Ƙira kantin maganinku a ƙalla kwana biyu kafin maganin ya ƙare don ƙarin siya.
- Ajiye hydroxyurea a ɗaki mai sanyi, a busasshen wuri, kuma nesa da rana. Kada a ajiye shi a ɗakin wanka ko ɗakin girki.
- Kada a riƙe magunguna waɗanda suka ƙare. Tuntuɓi mai saida magani game da yadda za a zubar da magungunan da suka ƙare.
Bayani akan shan magani fiye da ƙima
Kada a bar hydroxyurea a inda yaro zai iya gani ko taɓawa. A ajiye shi a wuri mai aminci. Idan yaronka ya sha hydroxyurea fiye da ƙima, ƙira cibiyar bayani game da guba ta wayar waɗannan lambobin. Ƙiran kyauta ne.
- Ƙira 1-844 POISON-X, ko 1-844-764-7669, daga kowanne yanki a Canada banda Quebec.
- Ƙira 1-800-463-5060 idan ka na zaune a Quebec.
Sanarwar nisantar alhaki: Wannan bayanin Med-aid na Iyali ya na da inganci a lokacin buga shi. Ya na ba da takaitaccen bayani game da hydroxyurea amma ba ya ɗaukar duka bayanan da ake buƙata game da wannan magani. Ba duka illoli aka lissafa ba. Idan ku na da tambayoyi ko ku na so ku san ƙarin bayani game da hydroxyurea, ku tuntubi likitan ku.