Mene ne ciwon ƙwayar halittar sikila (SCD)?
Ciwon ƙwayar halittar sikila (SCD) na ƙunshe da cututtukan jini waɗanda ke hana jini gudana yadda ya kamata a jiki.
Hemoglobin shi ne babban abu a cikin ƙwayoyin jini. Aikinsa shine taimakawa jini ɗaukar iskar oksijin daga huhu zuwa sauran sassan jiki. Akwai nau’ukan hemoglobin da dama, ciki har da hemoglobin A (na lafiya) da hemoglobin C da S (masu matsala).
Ƙwayoyin jan jini masu lafiya su na da yawan hemoglobin A, wanda ke sa su taushi da zagaye don su iya tafiya cikin sauƙi a jini. Amma masu ciwon ƙwayar halittar sikila na da yawan hemoglobin S (wanda ake ƙira sickle hemoglobin). Hemoglobin S ya na iya yin ƙarfi a cikin ƙwayoyin jini, ya na sa su zama kamar baka. Idan ƙwayoyin jini suka yi wannan siffar, ba za su iya ratsawa ta hanyoyin jini cikin sauƙi ba. Wani lokaci har ma su kan toshe hanya kuma ba za su kai iskar oksijin ga wasu sassan jiki ba.

Alamomi da Siffofin ciwon ƙwayar halittar sikila
Babban siffofin ciwon ƙwayar halittar sikila su ne yawan rashin jini da kuma maimaituwan toshewar hanyoyi na jini:
-
Rashin jini ya na faruwa ne idan babu isasshen hemoglobin ko ƙwayoyin jan jini a jiki. Idan wannan ya faru, isasshen oksigen ba zai isa ga jiki ba. Wannan na iya haifar da zama fari, gajiya ko rauni. Misali, yaro na iya gajiya fiye da abokan wasansa lokacin yin wani aiki. Ya na iya shan wahala wajen mai da hankali.
ƙwayoyin jini da suka yi siffar baka ba sa rayuwa kamar yadda mai lafiya ke rayuwa. Su na mutuwa da wuri, su na haifar da yawan rugurguza jini. Wani lokaci hanta ba ta iya fitar da waɗannan ƙwayoyin jinin da ya rugurguje a lokaci guda, kuma wannan na iya sa fararen idanu su zama rawaya daga lokaci zuwa lokaci.

- Yanayi na toshewar hanyar jini (vaso-occlusive episodes) yana nufin tarewar hanyoyin jini a kowanne sashin jiki saboda ƙwayoyin jinin da suke kama da siffar baka. ƙwayoyin jinin da suke kama da wannan siffar, ba sa iya tafiya a jiki yadda ya kamata kuma su na cunkushewa. Wannan ya na haifar da toshewar hanya da rashin iskar oksigen a sashin da abin ya shafa a jiki. Alamomin cutar su na dogara da inda hanyoyin jinin suka toshe. Idan hanya ta jini da ke zuwa ƙashin ƙafa ta toshe, to za a ji zafi a ƙafa. Idan kuma hanya ta jini da ke zuwa ƙwaƙwalwa ta toshe, to za’a samu alamomin cutar shan jini, kamar rauni a ɓangaren jiki guda.

Sauran matsaloli a cikin yara masu ciwon ƙwayar halittar sikila sun haɗa da ciwon ƙirji mai tsanani, kamuwa da cuta da kuma kumburin saifa (tsarewar saifa).
Lokutan ciwo
Alamar da aka fi gani a lokacin toshewar hanyar jini ita ce zafin ƙashi. Zai iya shafa kowanne ƙashi, ciki har da na hannu, ƙafa, baya da kai. Waɗannan lokutan su na da suna a turance "pain crises," kuma su na iya zuwa ba tare da wata alama ba. Wasu yara na iya fama da rashin lafiya kafin zafin ya fara, kuma su na iya sanar da manya.
Abubuwan da ke iya jawo zafin sun haɗa da:
- kamuwa da cuta
- damuwa/gajiya
- ƙarancin ruwa a jiki
- fitowa lokacin sanyi ko yanayin zafi sosai
Wasu lokutan zafi na iya faruwa ba tare da wani sanannen dalili ba.
Yadda Ake Hana Lokutan Ciwo
Za ka iya taimakawa wajen hana lokutan ciwo ta hanyar:
- Bayar da isasshen ruwa ga yaranka don su kasance ba tare da ƙishiruwa ba.
- Saka wa yaranka tufafi masu ɗumi da yawa a lokacin sanyi idan za su fita daga gida.
- Tura rigar sweatshirt da safa na ƙafafu a cikin jakar yaranka zuwa makaranta idan za su jiƙe a lokacin hutu ko wani lokaci.
- Sanin zazzaɓi a matsayin wata alamar cuta, kuma a kai yaron zuwa wurin likita nan-da-nan.
- Tabbatar da cewa yaron ya na guje wa motsa jiki mai nauyi ba tare da samun damar hutu da shan ruwa ba, musamman a ranakun zafi.
Duk da waɗannan hanyoyin, yara na iya samun lokutan zafi.
Yaya ake kamuwa da cutar sikila?
Cutar sikila (SCD) ta na da asali daga gado, wato ana gadonta a cikin iyali. Ba cuta ce mai yaɗuwa ba: ba za ka iya yaɗa ta kamar mura ba, kuma ba za ka iya kamuwa da ita daga wani ba.
Yawan Cutar Sikila
Cutar sikila ita ce cutar jini da aka fi gada a Amurka da Kanada. Ana samun ta fiye da yawa a tsakanin mutanen da suka fito daga Afirka ko yankin Karibiyan, amma yara daga Gabas ta Tsakiya, yankin Mediterranean, da Kudancin Asiya ma suna iya kamuwa da ita.
Magani
Duba Cutar sikila: Abin da za a yi idan ɗanka bai da lafiya don fahimtar yadda za ka taimaki ɗanka idan ba ya jin daɗi. Ka samu bayani akan:
- Zazzaɓi
- Gano ciwo
- Sarrafawa da kula da ciwo
- Magunguna
- Dabarun jiki
- Dabarun tunani
Idan mutum na da cutar sikila, aikin saifa ba ya inganci wajen kashe ƙwayoyin wasu ƙwayoyin cuta. Ya kamata a ba su ƙarin alluran rigakafi don kare su daga cututtuka da ƙwayoyin cuta na pneumococcal da meningococcal ke haifarwa. Idan ɗanka ya na ƙasa da shekaru biyar, ya kamata a ba shi maganin rigakafi na kariya. Mafi yawan maganin rigakafi da ake amfani da shi shine amoxicillin.
Zazzaɓi a cikin yaro da ke da cutar sikila ana ɗaukar sa gaggawa, kuma ya na buƙatar kulawa cikin sauri da maganin rigakafi. Zazzaɓi ya na nuna alamun kamuwa da cuta.
Dole ne a sami ma'aunin zazzaɓi a gida don auna yanayin zafin ɗanka idan ba ya jin daɗi. Idan zafin jiki ya fi 38°C a ƙarƙashin hannu ko ya fi 38.5°C a baki, dole ne a kai shi asibiti cikin gaggawa.
Magunguna irin su acetaminophen da ibuprofen su na rage zazzaɓi amma ba sa maganin cutar da ke haifar da zazzaɓin. Amfani da su na iya sa a jin sauƙi na ƙarya ko kuma a yi watsi da muhimmancin zazzaɓin. Waɗannan magunguna ya kamata a ba wa yaro ne kawai don rage zazzaɓi bayan an duba shi a wajen likita.
Bukatar Ruwa ga Yara Masu Cutar Sikila
Yara masu cutar sikila su na fitar da yawan fitsari fiye da takwarorinsu saboda ko da ba sa iya tsawaita narkar da fitsari.
Saboda haka, idan yaro ya na fitar da fitsari fiye da yadda aka saba, dole ne a ƙara yawan shan ruwa. Wannan abu ya na da matuƙar muhimmanci ga masu cutar sikila, saboda rashin isasshen ruwa na iya jawo ciwon sikila. Idan yaro mai cutar sikila ya rasa ruwa a jikinsa, ƙwayoyin jinin sa ma za su bushe kuma su canza siffa, suna toshe hanyoyin jini kuma su na haifar da zafi mai tsanani. Ka tabbata cewa ɗanka ya na da sauƙin samun ruwa a kowane lokaci.
Sauran Magunguna da Jiyya don Cutar Sikila
Ɗanka na iya karɓar magungunan cutar sikila a asibiti don hana matsaloli da kuma shan magunguna da za su yi aiki akan ƙwayoyin sikila, cututtuka, da ciwo. Don ƙarin bayani game da waɗannan jiyya, duba Cutar sikila: Nau'in jinya da magunguna.
Yanayi na Musamman da Ya Kamata Iyaye Su Kira 9-1-1
Idan ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan ya faru, nemi kulawar gaggawa ko kira 9-1-1 nan da nan:
- Wahala wajen numfashi
- Rashewa ko rashin sani
- Matsananciyar ciwon kai
- Wahala wajen magana ko murya mai sarƙaƙiya
- Rashin ƙarfin hannaye ko ƙafafu
- Faruwar fashewar jijiyoyi
- Zazzaɓi fiye da 39°C
- Rashin kuzari ko barci mai yawa ba tare da dalili ba
- Amai mai ci gaba
- Gane cewa saifa ta yi girma